Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero Ya Jagoranci Bikin Murnar Fara Aikin Jigilar Matafiya Na Jirgin Qatar Airways a filin Jiragen Sama na Malam Aminu Kano.
Wannan Shine Karon Farko Da Jirgin Qatar Airways Ya Fara Sauka a Filin Sauka Da Tashin Jirage Na Mallam Aminu Kano.
Jirgin dai ya sauka a Kano ne a yau Laraba, Wanda kuma shine karon farko da Kamfanin ya fara sauka a Jihar Kano, duk da kasancewar Jihar cibiyar kasuwanci ta Kasar.
Al’ummar Jihar da dama ne suka bayyana Farin cikinsu da zuwan wannan jirgi Jihar Kano, suna masu fatan zuwan sa zai kawo ci gaba maras misaltuwa ga tattalin arzikin Jihar.
Comments 1