Wani jirgin ruwa dauke da Baki haure 27 ya nutse a takeun dake tsakanin Turkiyya da tsibirin Chios na kasar Girka a ranar Talata.
Jami’an tsaron gabar tekun Girka sun sami nasarar ceto mutane 20 cikin wadan lamarin ya shafa.
Gidan rediyon kasar Girka ERT ya ruwaito cewa, mutane bakwai ne har yanzu ba a gansu ba, kamar yadda ma’aikatar tsaron gabar ruwan kasar ta ruwaito.
Jirgin ruwan NATO, jirage masu saukar ungulu guda biyu da jiragen ruwa masu tsaron gabar teku da dama da kuma jiragen ruwa da ke wucewa suna cikin aikin ceto a tekun yanzu haka.
KARANTA WANNAN LABARAN: Samarwa Matasa Aikin yi Zai Rage Matsalar Tsaro a Nigeria
Kafofin yada labarai na kasar sun ruwaito cewa iska mai karfi na kawo cikas ga binciken.
A wani labarin Kuma na daban.
Tsohon shugaban Koriya ta Kudu, Roh Tae-woo ya rasu yana da shekaru 88 a duniya, kamar yadda mukarrabansa suka bayyana.
Mataimakan sun ce Roh, wanda ya rike mukamin shugaban kasa daga shekarar 1988 zuwa 1993, kwanan nan aka kwantar da shi a asibiti bayan da rashin lafiyarsa ya tabarbare.
Roh, wanda tsohon janar ne, ya gaji tsohon shugaban kasar Chun Doo Hwan bayan ya taimaka masa ya kwace mulki ta hanyar juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 1979.Juyin mulkin dai wanda ya cike gibin iko da mutuwar tsohuwar shugabar gwamnati Park Chung Hee ta haifar.
Yayin da zanga-zangar neman dimokuradiyya ta yadu a fadin kasar a shekarar 1987, Roh ya amince da kiraye-kirayen tsarin shugaban kasa kai tsaye kuma an zabe shi a matsayin shugaban kasa daga baya a waccan shekarar ta hanyar jefa masa kuri’a kai tsaye.
A wani yunkuri na ganin ya zubar da kimarsa na soja, Roh ya fara gudanar da mulkinsa da taken bude zamanin talakawa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, A shekarar 1996, Roh da Chun an same su da laifin cin hanci da rashawa da kuma tada kayar baya saboda rawar da suka taka a juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 1979 da kuma murkushe masu fafutukar tabbatar da dimokradiyya a shekarar 1980 a birnin Gwangju na Kudu maso yammacin kasar.
An yanke wa Roh hukuncin daurin shekaru 17 a gidan yari kuma ya fuskanci tarar dala biliyan 260 da (dala miliyan 223) inda aka yi masa afuwa a shekarar 1997.