Wani jirgin sama Kiran AN-26 na kasar Rasha, mai dauke da akalla mutum 28 ya bace bat, a yankin Kamchatka dake gabashin kasar. Kamar yadda kafafen yada labaran Kadar suka bayyana.
Jami’an gwamnatin kasar sun bayyana cewa, jirgin na hanyar Petropavlovsk-Kamchatsky ne aka daina samun bayanan shi ta Na’ura Mai Kwakwalwa.
Kafar yada labarai na Aljazeera ya ce, lamarin ya faru ne a yau Talata.
Kazalika ana samun rahotanni mabanbanta kan abinda ya haddasa bacewar jirgin, inda wata majiya ta bayyana wa TASS cewa, da yiwuwan jirgin ya fada cikin teku, yayin da wata majiyar daban ta ce, yankin Interfax Xewa jirgin ya fadi, kusa da garin Palana.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Kaduna ta Rufe Makarantu 13
A karshe rahotanni sun nunar da cewa, Mahukunta kasar ta Rasha sun an kaddamar da wani kwamitin da zai gudanar da binciken gaggawa domin nemo jirgin.
Comments 2