A kalla mutane 45 ne suka gamu da ajalinsu sakamakon hatsarin Jirgin saman sojin kasar Philippines, yayin da aka zakulo gwamman was da rai.
Jirgin yana dauke ne da mutane sama da 90 inda galibinsu sojoji ne sa’ilin da ya kauce hanya a tsibirin Jolo.
Ma’aikatar tsaron kasar ta ce galibin wadanda suka mutun jami’an soji ne, yayin da aka samu uku daga Fararen hula dake kasa suka ce ga garinku.
Jirgin ya kama da wuta ne a sararin samaniya, lamarin da ya sanya samaniyar ta yi duhu tamkar ba duniya ba.
Rahotanni sun bayyana cewa an ga jami’an sojin na ta tsalle suna ficewa daga jirgin, ko da yake babu wani karin bayani game irin dabarar da suka yi amfani da wajen ficewar.