Rundunar Sojin Saman Nigeria a ranar Asabar tace jirgin ta, ya kashe ƴan ta’adda da dama wanda suka taru domin yin wani taro a Island ta Tumbuns na Lake Chad da kuma Malam Fatori.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Saman Nigeria Edward Gabkwet ya bayyana haka a ranar Asabar da safe.
Yace Sojin Saman Najeriya ta samu bayanan sirri a ranar 20 ga watan Oktoba cewar kimanin tawaga 20 cikin jirgin ruwa na ƴan Boko Haram/ISWAP zasu yi taro a wurin.
KARANTA WANNAN LABARIN: “Ana kai wa Jami’anmu Hari” inji Hukumar Kwastom
A cewar sa, biyo bayan samun bayanan sirri, Sojan Rundunar Sojin Ƙasa dake aiki a ƙarƙashin aikin Operation Haɗin Kai sun kai hari a wurin.
“Dayake isa wurin, matuƙin jirgin ya lura da jiragen ruwa guda 20 ɗauke da ƴan ta’addan guda 5-7,” inji shi.