Rundunar sojin saman Nigeriya ta sanar da cewa jirgin yakinta ya yi hatsari yayin da yake tsaka sa luguden wuta kan yan fashin daji.
Rundunar ta ce jirgin nata na aiki ne tsakanin iyakar Jihar Kasuna da Zamfara sa’ilin da ya yi hatsarin.
A wata Sanarwa da Daraktan Yada labaran rundunar Air Komado Edward Gabkwet ta ce matukin nata mai suna Flight Lieutenant Abayomi Dairo ya yi nasarar auna arziki ne bayan da ya yi kokarin tsalle daga jirgin tare da tallafin wasu jami’ai.
Sanarwar ta kara da cewa Abayomi ya yi ta zillewa wa yunkurin yan fashin daji na ganin sun ga bayanaa, inda har ya yi nasarar garzayawa sashen kula na rundunar sojin Najeriya.
Sai dai rundunar sojin ta ce wannan yunkuri ba zai kashe mata gwiwa ba wajen tabbatar da Kudirin shugaban kasa Muhammadu Buhari na yaki da yan ta’adda.
Idan ba a manta ba a yan baya bayan nan ne shugaba Buhari ya bada umarnin yin ko a mutu ko a yi rai kan yan ta’adda sa auka addabi yankunan Zamfara da Katsina da kuma Kaduna.