Wani jirgin yakin sojin Nigeria ya hallaka yan bindiga da dama, a wani ginin makaranta dake karamar hukumar Shinkafi na jihar Zamfara a jiya Lahadi.
Jirgin ya kuma Kai samame ta sama a yankin Zangon Dammaka da Jajaye, inda shugaban yan bindiga Kachalla Haru da magoya bayan sa ke boye.
Wata majiya ta karkashin kasa ta bayyana wa kamfanin dillancin labarai na PRNigeria cewa, rundunar hadaka dake aiki a Zamfara ce ta jagoranci wannan samamen a karshen makon da ya gabata.
Shaidan ya bayyana cewa, ” A jiya Lahadi 29 ga watan Augustan shekarar 2021 da misalin karfe 2 na rana, Munsami wani sahihin bayani dake cewa, yan bindiga sama da 100 sun yi wa wani ginin makaranta kawanya a kwauyen Gidan Rijiya na garin Galadi, dake keramar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara”
KARANTA WANNAN LABARIN: An rufe hanyar Kano zuwa Jigawa na wucin gadi, inji FRSC
” Hakan yasa rundunar hadaka ta Operation Hadarin Daji, ta tada jirgin Saman sojin Nigeria domin Kai samame a yankin, inda hakan yasa akyi nasarar kashe wasu yan bindiga da dama, da kuma lalata musu makamai” inji shi
Kazalika jirgin Saman ya Kkai samame maboyar Halilu Tubali dake dajin Subulu.
Sai dai haryanzu ba’asan yawan yan bindigan da rundunar ta yi nasarar kashe wa ba, Amma shaidan ya ce, an kashe akalla guda 50 da kuma kone musu Babura a kyauyen Gidan Rijiya.
Sai dai kamfanin Dillancin labaran ya ce, ya yi kokarin ji ta bakin jami’in Hulda da jama’a na rundunar soji saman Nigeria Air Commodore Edward Gabwet, amma wayar shi ta ki shiga.