By Abbas Yakubu Yaura
Sojojin sun kawar da fargabar cewa jiragen yakin Super Tucano guda 12 da kasar ta samu kwanan nan zasu iya fuskantar hari da ga wasu ‘yan bindiga inda ake ajiye dasu.
Indan za’a iya tunawa Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa wani dan majalisar wakilai, Jafaru Muhammad, a zaman majalisar da aka gudanar a ranar Talata, ya yi gargadin cewa ‘yan bindiga zasu iya kai hari tare da lalata jiragen yakin da Amurka ta kai wa Najeriya kwanan nan.
Da yake gabatar da kudiri mai taken, ‘Akwai bukatar magance hare-haren ‘yan bindiga a mazabar tarayya na Agwara/Borgu a jihar Neja, ‘yan majalisar sun kara da cewa, “Majalisar ta kara nuna damuwa kan jiragen yaki na Super Tucano na Najeriya, wadanda suke ajiye Makarantar horarwar makamin Air 407 dake New Bussa a Jihar Neja, na fuskantar barazanar rugujewa, ganin yadda ta ke da kusanci da wurin da ‘yan bindiga ke boye a dajin Kainji dake dajin Borgu.”
A sakamakon haka ne gidan ya amince da kudirin.
Sai dai masana harkokin tsaro da suka yi magana a wata tattaunawa daban-daban da wakilinmu sun bukaci sojojin dasu tabbatar an kare lafiyar jiragen yakin.
Wani masani kan harkokin tsaro da leken asiri, Adamu Kabiru, yace da magabatan ’yan bindigar, bai kamata a yi wa alamar da Muhammad ya yi da safar hannu na yara ba.
Ya ce, “Wannan damuwa ce ta gaske. Ba mu cikin shakku kan karfin wadannan ‘yan fashin.
Kazalika yace ya kamata a motsa jirgin zuwa wurare mafi aminci, Na fi damuwa da filayen jirgin Abuja da Kaduna. Akwai bukatar hukumomi su kara kaimi. ‘Yan ta’addan suna kara karfin gwiwa.
A nasa bangaren, wani tsohon mataimakin darektan ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Mike Ejiofor, yace bai kamata a ce ana tattauna irin wannan batu a fili ba.
A cewarsa, kamata ya yi dan majalisar wakilai ya tuntubi shugaban hafsan sojin sama ko kuma ma’aikatar harkokin wajen Amurka kan lamarin.