Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya tabbatar da cewa; har yanzu yana cikin ‘yan takarar da suke neman kujerar gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 10 ga watan Oktoba.
Hakan na zuwa ne bayan jita-jitar da aka rika yadawa akan cewa ba ya cikin wadanda za su gabatar zaben fidda gwanin gwamnan na APC a ranar 20 ga watan Yuli.
An dai tantance wadanda za su yi zaben fidda gwanin ne a ranar 8 zuwa 10 ga watan Yuli a Abuja, inda ‘yan takara 12 za su fafata a zaben fidda gwanin gwamnan jihar.
Mr Ojo Oyewamide, babban mashawarci na musamman kan harkokin watsa labarai ga gwamnan, a sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi a garin Akure, ya ce makiya ne kawai suke yada jita-jitar domin kautar da hankalin magoya bayan Gwamna Akeredolu.