Najeriya da yiwuwar ta fuskanci ƙarancin Man Fetur, a yayinda Ƙungiyar Ƴan Kasuwar Man Fetur Masu Zaman Kansu IPMAN suka ƙi sayen man fetur daga ƴan kasuwa, wanda suka ƙara farashin litar man fetur daga 148 zuwa 157.
Mataimakin Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa Alhaji Abubakar Maigandi yace bambancin Naira 9 a duk lita ɗaya, wanda ƙari ne da kaso 6.08, ya haddasa rashin sayen man fetur ɗin.
Ya bayyana cewar, ƴan kasuwar sunyi burus da batun ɗaukar kayayyakin, tun bayan da Gwamnatin Tarayya ta hana su sayar da man fetur ɗin sama da yanda aka sanya farashi na tsakanin 162 zuwa 165 a duk lita ɗaya.

KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Bututun Iskar Gas na Kwarara a Legas
Wannan yanayi ya bada damar yiwuwar samun ƙarancin Man Fetur a wasu wuraren da ake saida man fetur, inji shi.
Maigandi ya kuma ƙara dacewar ta zaɓi yin taro da Hukumar Kula da Tashoshin Man Ruwa da Shugaban ta Ahmed Farouk.
Yace ƙungiyar zata buƙaci Hukumar ta baiwa mambobin su na samun kason su kai tsaye, maimakon dogara da wani mutum can daban.
“Idan kaje, zaka ga dogon layi ya fara samuwa, domin ƴan kasuwa sun ƙara farashin man fetur ɗin.
Haka zalika, Kamfanin Man Fetur na Ƙasa wato-NNPC ta cire tsoron da mutane keyi na samun ƙarancin man fetur.
Dayake jawabi a waya tarho, Daraktan na ɓangaren harkokin Al’umma Malam Garba Deen Muhammad yace “muna isasshen man fetur da zai kai kwanaki 30. Idan akwai yiwuwar samun wata matsala to ba dole bane.”