Jodan Sancho zai zo Manchester United kan yar jejeniyar kudi miliyan 73
Dan wasa Jodan Sancho ya rattaba hannu ga kungiyar kwallon kafa ta Manchester United shekaru biyar kan yar jejeniyar kudi miliyan 73.
KARANTA:-Ku gama zumudinku jam’iyyar APC ba za ta wuce 2023: Inji PDP
Tun baya kungiyar Manchester ke nuna bukatarta kan Dan wasan sai bana da Kungiyar Dotmund ta kudiri saida Dan wasan.
Dan wasan dai a halin yanzu yana cikin masu buga kasar cin kofin turai tare da Kasar ta Ingila, kawo yanzu dai Dan wasan kwallon mintuna shida kacal ya buga.
Sancho na so a bashi lamba bakwai a Manchester United amma haryanzu ba’a tsayar da lambar da zai goya ba.
Solskjaer mai Jan ragamar kungiyar Manchester United yana son kara sayon dan wasan baya na kungiyar Athletic Madrid.