Kasar Koriaya ta Arewa ta sha alwashin kara damara ga rundunar sojin ta biyo bayan kalaman shugaban Kasar Amurka Joe biden kan kalaman shi na nuna rashin amincewa dangane da gwajin makamin Nukiliya da Koriyan ta yi.
Kasar Koriya ta Arewa ta yi kaurin suna wajen gwaje-gwajen makamai masu linzami a wani mataki na tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro.
Pyongyang ta nuna halin ko oho ga Shugaba Biden ta inda ta nuna ba ta san ma an yi sabon zabe a kasar amurka ba.
To sai da ranar Alhamis din nan ta harba makamin ta mai linzami guda biyu izuwa tekun Japan da aka fi sani da East Sea dake yankin na Koriya.
Kuma biyo bayan wannan gwaji ne nan da nan Biden ya yi kakkausar suka dangane da matakin inda ya ce hakan karya yarjejniyar Majalisar Dinkin Duniya ce ta tsagaita wannan mataki, inda ya ja kunnen Koriya da ta kiyayi kan ta don gudun martani idan ta zabi hakan.
Amma Jami’i dake lura da shirin gwajin makamin Koriyar ri Pyong chol ya ce kalaman Biden din ya fara bayyana wa duniya wanene shi.