Shugaban Kasar Amurka Joe Biden ya soke duk wata doka da Tsohon Shugaban Kasar Joe Biden ya kafa kan hukunta masu wargaza kayan gwamnati a bainar jama’a, ciki har na mutum-mutumi.
Shugaba Trump ya sanya dokar ne a shekarar da ta gabata biyo bayan wata mummunar zanga-zanga da ta yi sanadiyar salwantar gumaka da dama.
Kazalika Biden ya dakatar da shirin da Trump din ya yi na gina gumaka don nuna mubaya’a ga yan mazan jiya.
Ba wannan kaɗai ba,Mista Biden har wa yau ya soke dokar haramta wa bakin haure zuwa shiga kasar don neman inshoran lafiya.
A watan Yunin Shekarar da ta gabata ne, Mista Trump ya sanya doka mai tsanani kan duk wanda aka kama yana ɗaiɗaita wani mutum mutumi.