Shugaban Kasar Amurka Joe Biden ya zama abin tsegumi a kafafen yada labarai bayan da bayan da ya yi ta fadiwa yayin hawa jirgin sojin kasar Amurka mai matakala guda.
Wani faifan bidiyo ya nuna yadda Mista Biden mai shekaru 78 yana ta tuntube yana fadiwa har sau uku yayin hawa jirgin sa na musamman.
Wannan Ibtila’i dai ya faru da Mista Biden ne yayin da yake shirin halartar wata ganawa da shu8gabannin yankin Asia da Amurka a birnin Atlanta da Georgia.
To sai dai wannan fadiwa bai hana shi yin katabus ba ina nan da nan ya tashi ya kade jikin shi ya hau jirgi ya yi gtaba.