An yi jana’izar tsohon Shugaban KAsar Tanzania John Magafuli a kauyen shi dake Gundumar Chato.
A makon jiya ne dai Mista Magafuli ya riga mu gidan gaskiya salamaon abin da aka bayyana da cutar zuciya.
Jana’izar wacce aka watsa kai tsaye a kafar Talabijin ya samu halartar yan uwa da abokan arziki da manyan jiga-jigan gwamnati bisa jagorancin Sabuwar shugabar Kasar Samia Suluhu Hassa.
An kuma harba bindiga har sau ashirin da daya a saman kabarin shi da wani jirgi ya yi shawagi jim kadan bayan jana’izar.
Mista Maqgafuli wanda aka zabe zuwa kan karagar mulki a shekarar 2015 shine Shugaban Kasar Tanzania na Farko da ya mutu yana kan karagar mulki tun bayan samun yancin kasar kimanin shekra sittin da ta gabata.
ra’ayoyi sun banbanta tsakanin yan kasar bisa irin shugabancin Mista Magafuli inda wasu ke cewaza a rika tuna shi da irin yadda ya yaki rashawa da cin hanci da kuma maida hankalin kan kula da arzikin kasa da Allah Ya hore wa kasar da kuma kirkiro da manyan ayyuka.
Yayin da a hannu guda ke cewa za a rika tun shi ne da irin yadda yake da zafi kan yan adawa da musguwa kafafen yada labarai masu zaman kan su da kuma kungiyoyi masu ranjin kare hakkin dan Adam.
Gabannin mutuwar Magafuli sai da ya caccaki gaskiyar lamarin annobar Korona inda ya ce nuna shakku a kain haka to sai dai ya janyo mishi suka daga manyan kwararrun lafiya daga fadin duniya.