DIMOKURADIYYA: Babban mai shari’a na kasa, Mai shari’a Tanko Muhammadu ya rantsar da Mai shari’a John Tsoho a matsayin mukaddashin babban alkalin babbar kotun gwamnatin tarayya. Sanna sai ya bukace shi ya yi irin aikin da wanda ya gada ya yin a bunkasa babbar kotun ta kasa. Babban Mai shari’ar ya kuma shawarce shi da ya dinga zagaya sassan kotun domin ya ga abin da ke gudana, sannan kuma, sannan kuma ya zabi zakakuran alkalai wadanda gudanar da ayyukansu kamar yadda suka kamata. “Akwai nauyi mai yawa da ya doru a kanka, na ganin ka zabi alkalan da suka dace wadanda za su gudanar da ayyukansu kamar yadda ya kamata. “Kotunka ita ce matattara ayyuka. Duk wanda duk wanda aka zaba ya je wurin dole ya yi sirin yin aiki tukuru.” Babban Mai shari’ar ya kara da cewa, ya zama wajibi mukaddashin babban alkalin ya nemi hadin kan sauran alkalan kotun, kuma ya tabbatar da yana ba dukkan ma’aikata hakkokinsu yadda za su ji dadin gudanar da ayyukansu.