Yayin da ake ta ikirarin komawar sa kan mulki, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana dalilin da ya sa ba zai sake tsayawa takarar shugabancin kasa ba.
Jonathan ya ce ba zai iya sake tsayawa takarar Shugaban kasa ba saboda an kore shi daga karagar mulki a zaben 2015.
KARANTA WANNAN LABARIN: Na Garzaya Kotu Don Ta Tabbatar Da Gwamnan Legas A Matsayin Mahaifina – Wani Matashi
Tsohon Shugaban kasar ya ce zai kaskantar da kansa ne ta hanyar siyan Fom tare da fara neman jan hankalin mutane ta hanyar sake yakin neman zabe.
Ya bayyana hakan ne a cikin wani littafi mai suna ‘My Time As Chaplain in Aso Rock’ wanda Nathaniel Bivan ya rubuta, ya kuma yi cikakken bayani kan tarihin Babban Faston Cocin Aso Rock Villa a zamanin Jonathan, Obioma Onwuzurumba.
An gabatar da littafin ga jama’a a ranar Talata.
Sai dai da yake tsokaci a kan kungiyar da ta sai masa fom din takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a kan Naira miliyan 100, Jonathan ya ce ya ji dadin lamarin amma ya dauki tamkar wani wasan kwaikwayo domin ba zai sake zama shugaban kasa ba.
Wata kungiyar makiyaya da almajirai ne dai suka saya wa Jonathan fom din tsayawa takara a APC Naira miliyan 100 gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Jonathan ya ce, “Na ji dadin lamarin wanda yake tamkar wasan kwaikwayo.”
“Idan kun tashi gobe kuma ku ga cewa ni ne Shugaban kasa kuma, hakan na nufin akwai yiwuwar an sami wasu yanayi da suka fi karfina. Amma ba wai a naje na sai fom din wata jam’iya, na fara rarrashin jama’a da yin yakin neman zabe ba, ko a PDP ne ko kum a Jam’iyar APC. Ba zan iya sake yin hakan ba; idan na yi haka, na rage kima na”
A wani labari kuma, Kano: Hadimin Shugaba Buhari Yayi Rashin Nasara a Kotu
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano karkashin jagorancin mai shari’a A.A Liman a ranar Larabar da ta gabata ta yi watsi da karar da hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya shigar.
A cikin karar yana kalubalantar nasarar Abdullahi Mahmud Gaya a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC na mazabar Gaya/Ajingi/Albasu a ranar 25 ga Mayu, 2022.
A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Liman ya ci gaba da cewa mai shigar da karar ya kasa tabbatar da zargin buga kuri’u da dama, wanda ya hana wakilansa 85 ‘yancin shiga wurin zaben.
Hakazalika kotun ta ce wanda ya yi zargin dole ne ya bayar da hujja ba tare da kokwanto ba, yana mai jaddada cewa wanda ya shigar da karar ya gaza sauke nauyin da ke kan kafadarsa a matsayinsa na mai kara.
Idan dai za a iya tunawa Abdullahi Mahmud Gaya ya samu nasara ne da kuri’u 109 a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a kananan hukumomin Gaya/Ajingi/Albasu