Mai horas da ƙungiyar ƙaallon ƙafa ta Liverpool wanda sunansa ya shiga kundin tarihin ƙungiyar ya cimma wani tarihi da Liverpool ta taɓa kafawa a shekaru sama da 40 abaya.
Ya cimma wannan tarihinne bayan ya lashe wasa a filin wasa na Anfield dake birnin na Liverpool a wasan mako na bakwai na gasar ta ajin Firimiyar ƙasar Ingila. Inda Liverpool ta lashe West Ham daci 2 da 1.
Liverpool dai ta kafa tarihin lashe wasanni 63 a gasar Firimiya a filin wasa na Anfield batare da ansami nasara a kanta ba daga shekarar 1978 zuwa 1980.
Shima haka a jiya Jurgen Klopp ya sake cimma wannan tarihi inda ya fafata wasanni guda 63 a gida batare da ansami nasara akanta ba. Ana ganin idan har Jurgen Klopp ya sake cin wani wasan a gida to ya kafa sabon tarihi a ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Liverpool.