Kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta raba gari da kocinta André Pirlo bayan da ya shafe kasa da shekara guda a Ƙungiyar.
Cikin yanayi irin na ban mamaki ne dai Pirlo ya maye gurbin Mauricio Sarri a kakar da ta gabata, to amma ya haramta wa Ƙungiyar lashen gasar “Serie A” a karon farko tun 2012.
Ana kiki-kaka ne dai a ranar karshe na kammala gasar Serie A din Juventus ta samu dakyar da jibin goshi ta tsallake zuwa gasar zakarun turai na baɗi.
A yanzu haka ana ganin tsohon kocin kungiyar Massimilliano Allegri ne zai sake hadewa da tawagar ta Turin a karo na biyu bayan da ya ajiye aikinsa a 2019.
A wani sakon da Juventus din ta fitar ta jinjina wa irin kokarin Pirlo a Ƙungiyar.
Korar Pirlo dai ita shine labari mafi kama hankali a duniyar kwallon kafa a bangaren da ya shafi bankwana da kocawa bayan Antonio Contw ya ajiye aikin horas da Inter Milan bayan lashe kofin Serie A, sai kuma na Zinedine Zidane sa shi ma ya bayyana ajiye nasa aikin a jiya Alhamis