Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA da ta kwarar ta ta Nahiyar Africa wato CAF, sun amince da dage wasa tsakanin Guinea da Kasar Morocco da aka tsara buga wa a yau Litinin, a wasan neman gurbin zuwa gasar cin Kofin duniya na shekarar 2022.
Sun yanke hukuncin dage wasan ne sakamakon juyin Mulki da rundunar sojin Kasar da ke yammacin Africa kuma Mai masaukin baki su kayi a jiya Lahadi, tare da tsare Shugaban kasar Alpha Conde.
A cikin wata sanarwa da tagwayen hukumomin su ka fitar, sun nuna cewa, “Yanayin siyasa da kuma tsaron kasar Guinea na Tangal-Tangal, Wanda hukumomin suka lura da hakan,j wajan dage wasan.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Sojoji sun yi Shugaban Kasar Guinea Juyin mulki
“Domin tabbatar da kiyaye lafiya da tsaron Yan wasa da kuma jami’an wasan daga hukumar FIFA da na CAF, mun amince mu dake wasan neman gurbin zuwa gasar cin Kofin duniya na shekarar 2022 tsakanin Guinea da Marocco.” Inji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa,” Kafin dage wasan an tsara buga shine a Conakry babban birnin kasar Guinea a yau Litinin”
A karshe hukumomin na FIFA da CAF sun ce, da yuwuwar su bayyana bayanan sanya wani lokaci, da za’a buga wasan a yammacin yau Litinin.