Jyoti Amge ita ce ‘yar kasar indiyar da ta shiga cikin littafin tarihi na Guiness a shekarar 2009, inda aka tabbatar da cewa ita ce mace mai rai mafi gajarta a duniya kasancewar tsawonta 61.95cm, wato sawu biyu, guiness world record ta ruwaito.
Bayan shekaru biyu, lokacin ta cika shekaru 17 a duniya, an kara gwada tsayinta inda aka gano ta k su 62.8cm wato sawu biyu da inci 0.72, hakan yasa aka kara tabbatar da cewa ita ce mace mai rai mafi gajarta a duniya.
KU KARANTA: Wata mata mai juna biyu ta nemi Naira 30,000 a hannun tsohon mijinta
Yanzu shekarunta 28, inda fiye da shekaru goma da gwada ta tana nan da tsawon da aka san ta da shi.
Yanzu tana shiga shirye-shirmen finafinai inda har ta fito a wani fim din dodannin Amurka mai suna Freak Show wanda aka haska a ranar 8 ga watan Oktoban 2014.
Duk da kankantarta, Joyti ta samu daukaka mai tarin yawa sannan a ko wanne lokaci ta kasance taba yawan murmushi da dariya.
Bella Hadid: Mace mafi kyau a duniya
Bella Hadid ita ce macen da aka zaba a matsayin mace mafi kyau a duniya bayan an yi nazari akanta bisa amfani da kimiyya, Legit.ng ta ruwaito.
Wannan sakamakon binciken ya dauke hankali kwadayi wanda mutane su ka hau guna-guni. Mutane da dama na kallon an kuranta Bella ne amma akwai fitattun matan da aka sani wadanda su ka zarce kyau da komai.
Kamar yadda kimiyya ta nuna, Bella Hadid ce mace mafi kyau a duniya kamar yadda @SaycheeseDGTL ya nuna inda ya bayyana kirar fuskar Bella.