Ka ɗora Jihar Kaduna a turba mai kyau – Sakon Uba Sani ga El-Rufa’i domin murnar zagayowar ranar haihuwar sa
Ɗan Takarar Gwamnan jihar Kaduna a karkashin Jam’iyyar APC Sanata Uba Sani ya taya murnar zagayowar ranar haihuwar Gwamna El-Rufa’i, inda ya yayi mashi addu’o’in samun cigaba.
Dan takarar gwamnan jihar Kaduna Senata Uba sani ya bayyana hakan ne a sakonsa na Taya murnar zagayowar ranar Haihuwarsa gwamna El’rufa a shafin sa na Facebook.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari Yana Kokarin Kawo Cikas Ga Dimokuradiyyar Najeriya Wajen Sake Fasalin Naira – Ganduje
Yace “Barka da zagayowar ranar haihuwar mai girma shugabana, mai ba ni shawara kuma jagora, mai tafiyar da al’amuran yau da kullum Malam Nasir Ahmad El-Rufai.
“Ina gode maka bisa sadaukarwar da kake yi wa jihar Kaduna da Najeriya”.
“Kun sake fasalin tsarin mulki a jihar Kaduna tare da dora jihar mai albarka bisa turbar ci gaba mai dorewa. Muna alfahari da kasancewa tare da kai” Uba Sani ga El-Rufa’i.
A matakin kasa, kun nuna jagoranci kuma kun kasance a sahun gaba wajen fafutukar kare muradun jama’a. Jajircewar ku da sadaukarwarku sun ci gaba da zaburar da matasa da duk ‘yan Nijeriya masu muradin ingantuwar Nijeriya.
Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya ci gaba da yi muka jagora, Ya kare ka, Ya kuma kara muka kwarin guiwa yayin da kuke sadaukar da kan ka wajen hidimtawa jihar Kaduna da Nijeriya da kuma bil’adama Inji shi Sanata Uba Sani.