Sarkin Owa Obokun na Ijesaland, Oba Adekunle Aromolaran yayi kira ga Gwamnan Jahar Osun Adegboyega Oyetola daya ɗaga darajar Kwalejin Ilmi ta Jahar dake garin zuwa Jami’ar.
Oba Aromolaran Wanda yayi jawabin a harshen yarbanci a lokacin daya karɓi Gwamnan da Tawagar sa, wanda suka zo ziyar duba aiki a Maɓazar Ijesa ta Gwamnatin Tarayya, a fadar sa dake Ilesa, yace Al’ummar garin zasu maidawa gwamna Oyetola irin karamcin da yayi masu ta hanyar bada goyon baya ga sake zaɓar sa.
Uban Ƙasar wanda ya yaba da Ƙoƙarin Oyetola akan al’amarin, yace al’ummar yankin sun fara tattara kuɗi domin taimakawa Gwamnati, tare da tabbatar da cewa an ɗaga darajar Makarantar zuwa Jami’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jihar Kano Na Amfana Da Gudunmawar Masu Yiwa Kasa Hidima – Ganduje
Oba Aromolaran yace Oyetola yace shine Dan takarar da Al’umma suka sani a yankin, yayi kira a gareshi da yayi aiki akan abinda Al’ummar suke so, na ɗaukaka ɗarajar Kwalejin Ilmi zuwa Jami’ar.
Yace “Oyetola zai cin ye zaɓen Gwamna a karo na biyu. Ina roƙo ga Allah daya karɓa mana.
“Baka buƙatar ka ɓata lokacin ka kana roƙon Kuri’a a Ijesha Domin tuni kana da masoya. Kazo domin ƙaddamar da wannan fadar duk da cewa kana da ayyuka.
Dayake jawabi da farko, Oyetola ya shaidawa Sarkin cewa, yazo ne fadar shi domin neman Albarkar shi, ta la’akari da cewa mambobin APC tuni sun zo domin neman wa’adi na biyu a ofishi.