A daidai lokacin da jihohin Zamfara, Katsina, Sakkwato, Kaduna da Neja suka fara daukar matakan bai daya wajen magance ayyukan ‘yan fashin daji, Majalisar Dattawan Nijeriya ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ayyana ‘yan fashin dajin da suka addabi yankin arewaci maso yamma a matsayin ‘yan ta’adda, tare da ayyana yaki a kansu da gaggawa.
Majalisar har wala yau ta kuma bukaci a shafe ‘yan fashin dajin daga doron duniya ta hanyar fara tarwatsa wuraren fakewarsu da jefa musu bama-bamai.
‘yan Majalisar Dattijan Nijeriya har wala yau na kuma son shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana shugabannin ‘yan fashin dajin a matsayin wadanda ake nema ruwa a jallo, domin kamo su a hukunta su.
An amince da wannan matsaya ne bayan wani kuduri da daya daga cikin ‘yan majalisar Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir ya gabatar da hadin guiwar wasu takwarorinsa takwas.
Comments 1