Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci sojoji da sauran hukumomin tsaro su tabbata babu abin da ya hana gudanar da zaben gwamna a jihar Anambra wanda aka shirya gudanarwa a ranar 6 ga watan Nuwamba.
Mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, ne ya sanar da umarnin, bisa lura da hauhawar matsalar tsaro a yankin Kudu maso Gabas, sakamakon hare-haren ta’addancin da ake dangantawa da haramtacciyar kungiyar IPOB.
“Buhari ya ba da umarni cewa, babu dalilin a bari wani abu ya hana gudanar da zaben cikin nasara. Mutane na da ’yancin jefa kuri’a su zabi shugabanninsu. Babu wani mutum ko kungiya da za a bari su haddasa yamutsi ko kashe-kashe”, inji shi.
Ya ci gaba da cewa; “Shugaban Kasa ya fada wa sojoji da sauran hukumomin tsaro karara cewa su dauki duk matakan tabbatar da ganin an gudanar da zaben, ko da kuwa ta hanyar mamaye wuraren ne da jami’an tsaro.
“Akwai illoli da dama a bari masu tayar da kayar baya su hana gudanar da zabe; farko dai tsarin dimokuradiyya muke bi, na biyu kuma idan aka bari bata-garin suka hana gudanar da zabe, to wasu ma za su bi sahunsu a wasu sassan kasar nan,” inji Monguno.
Shi ma a jawabinsa kan zaben na Anambra, Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Maigari Dingyadi, ya ce a shirye ’yan sanda suke su tabbatar da tsaro a Jihar Anambra da ma sauran sassan Najeriya.