Wani mai fafutuka a Jamhuriyyar Oodua, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya yi kira ga gwamnatin Nijeriya da ta kwashe Fulani makiyaya daga yankin Kudu maso Yamma don hana karuwar tashin hankali.
Ya ce idan har makiyaya ba su bar Ibarapa ba zuwa ranar Juma’a, to za su fuskanci halaka. Igboho ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya watsa kwanan nan a kafafen sada zumunta
Ya ce bai damu da Nijeriya ba amma game da batutuwan da suka shafi ‘Oduduwa Nation’ kamar yadda ya yi kira ga sauran masu kishin kasa da su shiga gwagwarmayar kwato ‘yancin Oduduwa, galibi ana amfani da shi wajen magana kan Yarbawa gaba daya.
Da yake magana da Yarbanci, ya ce, “Ba zan iya tattaunawa kan kasar da ke yaudarar Yarabawa ba. Ya kamata Yarabawa mu taru wuri daya mu tura wadannan mutane filin ajiye motoci. Babu wanda zai yi mana. Sanatocin mu basa yin komai”, inji shi.
Igboho ya ce yana da tabbacin cewa Dattawan Yarabawa ba su ji dadin kashe-kashen ba, amma, ya kalubalance su da su yi bidiyon da suka yi alkawarin goyon bayan kashe makiyaya din, idan ba haka ba.