Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya yi kira ga abokin hamayyar sa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, da ya gargadi magoya bayan sa kan yada labaran karya.
Da yake magana a madadin Asiwaju, Daraktan yada labarai da sadarwa na kungiyar kamfen din Tinubu (TCO), Bayo Onanuga ya yi zargin cewa magoya bayan Obi na yada labaran karya ga jama’a, wanda ke bata sunan dan takarar APC.
Ku tuna cewa wani rahoto ya fito ta yanar gizo a kwanakin baya, cewa shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya rubuta wasika ga Asiwaju, inda ya bukaci ya janye daga kudurinsa na tsayawa takarar shugaban cin kasar nan ya kuma marawa Peter Obi baya.
Shugaban ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a hukumance, wanda ya karyata rahoton, inda ya kira labarin na karya, inda kuma ya bayyana cewa ya samo asali ne daga bata gari da nufin yaudarar jama’a.
Manyan Jami’an Amurka sun firgice, yayin da Rasha ta harba tauraron dan adam din Iran
Da yake mayar da martani, Daraktan yada labarai na TCO ya roki Obi da ya yi barranta kan sa da magoya bayansa da ke daukar labaran karya kan tsohon gwamnan jihar Legas.
“Mun kai matsayin da ya zama wajibi mu gaya wa Obi ya nuna jagoranci tare da kin amincewa da magoya bayansa da ke amfani da labaran karya a matsayin kayan aiki da gangan don yaudarar zukatan ‘yan Najeriya” in ji Onanuga.