Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Wakilai Ta Najeriya yayi kira ga Shugaban Ƙasa Muhammadu da yayi gaggawar ɗaukar matakin hana yunƙurin tsaida Zirga-zirgar tashin jiragen sama a Najeriya, yana mai cewa hakan zai ƙirƙiri matsaloli da dama ga rayuwar Ƴan Najeriya.
Shugaban na maida jawabi ne akan yunƙurin shiga yajin aiki da aka sanar da Ministan Sufuri Hadi Sirika, da kuma Darakta-Janar na Hukumar kula da Sufurin Al’umma, Musa Nuhu daga Kamfanonin Jiragen.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da-Dumi-Dumi: Shugaban Bankin AFDB Ya Sayi Fom Din Takarar Shugaban Kasa
Kamfanonin Jiragen Sama sun sanar da yunƙuri tsaida dukkanin Zirga-zirgar Jiragen Sama a Najeriya daga ranar 9 ga watan mayu na Shekarar 2022, sakamakon tsadar Mai, wanda ya tashi daga Naira 190 zuwa Naira 700 a duk lita ɗaya.
Bada sanarwar da Kamfanonin suka yi ya nuna cewa yunƙurin da Majalisar Dattijai da na Wakilai suka yi na hana hakan bai haifar da nasara ba.
Majalisar a ranar Litinin zata gudanar da wani taron gaggawa, ƙasa da mako guda, bayan ta ɗage zaman ta a ranar 24 ga watan mayu na Shekarar 2022, domin tattaunawa akan abubuwa masu mahimmanci.
Akawun Majalisar Dr Yahaya Dan zaria ya sanar da sake kiran zaman Majalisar a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Asabar.
Shugaban Marasa Rinjaye Ndudi a cikin sanarwar daya fitar a ranar Asabar ya zargi rikici a ɓangaren Sufuri da rashin maida hankali ga Gwamnatin APC ƙarƙashin jagorancin Buhari.