Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Asabar ya bayyana tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo a matsayin wanda za’a karanta a sha’anin Kishin Ƙasa.
A lokacin da yake taya shi murna akan cikar sa shekaru 85 a Duniya, Shugaban Ƙasa yace wanda ya siffanta da kishin Ƙasa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Najeriya da Ghana: Dole Super Eagles tayi taka tsantsan — Cewar Ndidi
Buhari ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya fitar ta taya murna daga bakin Mai Magana da Yawun sa, Femi Adesina mai taken “Buhari ya taya murna ga tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo da cikar shi shekaru 85 da haihuwa.
Sanarwar tace “Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yayi amanna dacewar tsohon Shugaban Mulkin Soji daga Shekarar 1976-1979 , tsohon Shugaban Mulkin Farar hula daga Shekarar 1999-2007 mutum da za’a karanci Kishin Ƙasa a gareshi, Shugabanci wanda ya sanya Ƙasar ta zamanto tana tsarin Dimokuraɗiyya a Shekarar 1979, kuma ya zama Shugaban Ƙasa a matsayin zaɓaɓɓe a Shekarar 1999.
“Shugaban Kasar ya tabbatar dacewa, irin ƙoƙarin Tsohon Shugaban Ƙasa zai cigaba da Kasancewa a tarihin Kasar.
Comments 1