Ƙungiyar Ƙabilun Yarbawa ta Afenifere ta buƙaci Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari daya ayyana ƴan bindiga a matsayin ƴan ta’adda, inda ta buƙace shi daya rabu da kiran da Malamin addinin Musuluncin nan keyi Sheikh Ahmad Abubakar Gumi.
Majiyar Jaridar dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar, Gumi a ƴan kwanakin nan ya gargaɗi Shugaba Buhari akan kada ya ayyana ƴan bindiga a matsayin ƴan ta’adda, inda yace hakan zai haifar da matsalolin da dama a ƙasar.

KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya Ta tabbatar da cewa, za ta yi Aikin Hanyar Gombe zuwa Biu
A wajen Gumi, ƴan bindiga dake kisa da garkuwa da rayukan da basuji ba su gani ba a wasu sassan ƙasar ya kamata a yafe masu, inda yake cewa suna yaƙi domin ƙwato ƴancin kan su.
Amma a wajen Afenifere bata amince da kiran da Gumi yake yi ba, inda take kira ga Buhari da Gwamnatin Tarayya data jefar da shawarwarin daya bayar gaba ɗaya.
Ƙungiyar tace bawai tana so a ayyana ƴan bindiga a matsayin ƴan ta’adda kaɗai ba, har da ɗaukar masu hukunci irin na ƴan ta’adda.
Afenifere tayi wannan jawabin a cikin wata takardar bayan taro wadda Sakataren Yaɗa labaru Jare Ajayi ya sanyawa hannu, a ƙarshen taron da suka yi na watan Oktoba wanda ya wakana a gidan mai ruƙon ƙwarya na Shuwagabancin ƙungiyar Chief Ayo Adebanjo a Sanya-Ogbo, Ijebu-Ode ta Jahar Ogun.
Ƙungiyar Ƙabilun Yarbawa ta bayyana rashin jindaɗi na yadda masu tada ƙayar baya, da ta’addanci da garkuwa da mutane, da sauran ayyukan ashsha ke cigaba da ƙaruwa, duk da ɓaɓatun da gwamnati take yi tana samun nasara a yaƙi da matsalar.
A lokacin da take bayyana rashin amincewa da yadda Gwamnatin Tarayya ke magance matsalolin tsaro, Afenifere tace tabi sahun Majalisun Ƙasar da sauran mutane, akan kiran da ake yi na “waɗanda suke ta’addanci da kashe-kashe a ayyana su a matsayin ƴan ta’adda.