Gabanin zaben shugaban kasa na 2023, Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya bukaci tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Ahmed Makarfi da ya tabbatar da cewa jam’iyyar ta yi nasara a jihohin Arewa.
Wike yace ya kamata Makarfi ya tabbatar da cewa PDP tayi nasara a jihohin Kano, Jigawa, Niger, da Kaduna.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa, Wike Ya yi wannan jawabi ne a wajen kaddamar da yankin Sandfilled Ogbunabali a Fatakwal, babban birnin jihar a ranar Talata.
KARANTA ANAN: Sanata Uba Sani Ya Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsakin Kananan Hukumomi 8 Na Kaduna
A nasa bangaren tsohon gwamnan Kaduna, Ahmed Makarfi ya bukaci yin duk mai yiwuwa wajen ganin wasu ‘yan takarar shugaban kasa sun koma jam’iyyar PDP.
Ya kuma bukaci jam’iyyar Labour Party, da dan takararta na shugaban kasa Peter Obi da takwaransa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Rabiu Kwankwaso da su koma PDP.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna yace Obi da Kwankwaso su hadiye burinsu su koma PDP, don tabbatar da Nasarar Jam’iyyar da Dan takararta.
A wani labarin kuma: Osinbajo Ya Tashi Zuwa Amurka, Domin Ganawa Da Kamala Harris, Da Sauransu
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a safiyar ranar Larabar nan ya tafi kasar Amurka domin neman hadin kan duniya da goyon baya ga shirin da Najeriya ta kaddamar da shi a kwanan nan.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande, ya fitar ta ce Osinbajo zai gana da takwaransa na Amurka, Kamala Harris; Kungiyar Bankin Duniya, da sauran abokan hulda.