Sanata Ekweremadu Ya Nemi Gwamnatin Tarayya Ta Yanke Huldar Jakadanci Da Afrika Ta Kudu.
Tsohon mataimakin shugaban majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ike Ekweremadu, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yanke huldar jakadanci tsakaninta da kasar Afrika ta Kudu.
Sanata Ike Ekweremadu ya nemi Nijeriya da a datse duk wata alaka ta kasa da kasa da ke tsakanin ta Afrika ta Kudu ne a dalilin sababbin harin da aka kai wa wasu ‘Yan Nijeriya da ke kasar wajen. Ike Ekweremadu ya yi tir da harin da ake kai wa mutanen Nijeriya a kasar ta Afrika ta Kudu.
Ekweramadu ya ce akwai jahilci da rashin kishin Afrika da butulci a game da hare-haren.