Wata Kungiya mai mubaya’a ga Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa Bola Ahmad Tinubu ta sha alwashin maka shi a kotu muddin yaƙi amincewa da bukatar tsayawa takara a shekara ta 2023.
Wannan barazana da su ka yi wa shugaban na APC na zuwa ne daidai lokacin da ake ta yamaɗiɗin cewa yana da muradin tsayawa takarar shugabancin kasar.
Kungiyar mai suna Disciples of Jagaba, gamayya ce ta Ƙungiyoyin siyasa sha biyu da na aladu, da ta tsaya kai da fata na ganin sai Tinubu ya zama Shugaban Kasar Najeriya a 2023.
A jawabinsa shugaban kungiyar ta Kasa Kwamared Abdulkareem Adegoke Alawuje ya ce a halin da ake ciki babu wani nagartaccen mutum da zai iya rike kasar nan fiye da Tinubu.
Ya ce muddin Tinubu ya ƙi amincewa da bukatar su, to lallai za su maka shi kotu din a tilasta mishi tsayawa takarar.
Har wa ya ya ce shi kaɗai ke da zummar da zai dora daga irin abin Alkhairin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aza tubalin shi.