An gargadi dan takarar shugaban kasa, jam’iyyar APC, Bola Tinubu, da ya yi hattara da Gwamna Nasir El-Rufai. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito
Deji Adeyanju, wani mai fafutuka a fannin zamantakewa da siyasa ne ya gargadi Tinubu da ya shirya domin El-Rufai zai ci amanarsa idan lokaci ya yi.
KU KARANTA: EFCC Ta Kwato Naira Miliyan 900 Na Shirin NHIS
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Adeyanju ya nuna cewa gwamnan ya ci amanar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Da yake jaddada cewa mulki na wucin gadi ne, Adeyanju ya rubuta: “ElRufai zai ci amanar Tinubu a daidai lokacin da ya dace. Buhari yana koyon sabbin darasi. Har yanzu bai bar Aso Rock ba amma sun riga sun nuna masa irin abun da mai yi tsammani ba. Koyaushe iko yana wucewa.”
El-Rufai wanda aka san yana da kusanci da Buhari ya yi magana kan shugaban da gwamnatinsa a makon jiya.
Jigon na APC ya zargi Buhari da barin miyagu su yi amfani da shi wajen yakar APC.
El-Rufai ya ce mutanen da ke amfani da shugaban kasa a matsayin makamin kayar da jam’iyyar APC na yin haka ne saboda sun kasa yin yunkurin tilasta samar da nasu dan takarar a jam’iyyar a zaben fidda gwani na watan Yuni 2022.
Gwamnan ya mayar da martani ne ga sanarwar da Buhari ya yi kan manufofin sake fasalin Naira da kuma matsalar kudin da ‘yan Najeriya ke fama da su.
A wani labari kuma, Na’urar BVAS Alheri Ce Ga Tsarin Zaben Najeriya – APC PCC
Kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, PCC, ya bayyana kwarin gwiwar cewa amfani da tsarin tantance masu kada kuri’a na BVAS, zai taimaka wajen kawar da siyasar kudi a zaben Najeriya.
Festus Keyamo, mai magana da yawun kwamitin PCC ne ya bayyana hakan a lokacin ganawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Abuja ranar Lahadi. Daily Post ta ruwaito.