Daga Sulaiman Musa
Gwamnan Jihar Rivers, Mistga Nyesom Wike, ya bukaci Ministan sadarwa da fasahar tattalin arziki, Malam Isa Pantami da ya gaggauta ajiye mukaminsa cikin ruwan sanyi biyo bayan zarge-zargen mara wa ta’addanci baya.
Gwamnan ya ce a irin wannan yanayin da ake ciki, bisa zargin da ake cewa Amurka ta sanya Ministan cikin wadanda idonta ke kansa kawai ya ishi ministan daukan matakin ajiye aikinsa.
A sanarwar da Kakakin gwamnan, Kelvin Ebiri ya fitar, gwamnan ya bayyana hakan ne a yau yayin da ke ganawa da gidan talabijin din AIT a Fatakwal da ke jihar Ribas.
Gwamnan ya nuna cewa shirun da gwamnatin tarayya ta yi kan wannan batun ma kawai ya ishi ya nuna wa duniya cewa gwamnatin ba ta damu da wannan lamarin ba.
Gwamnan ya ce, bai dace ba ko kadan gwamnatin da jama’a suka zaba bisa yarda ta bada kofa wajen marawa ko tausaya wa ‘yan ta’adda baya, ya nuna cewa tun da zargin na cigaba da yawo, ya kamata ministan ya sauka har sai an kammala bincike.