Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu ya bukaci gwamna Samuel Ortom na jihar Benue da ya shiga jirgin yakin neman zaben jam’iyyar, Daily Post ta rawaito.
Ayu ya ce idan Ortom ya hada kai da PDP zai tabbatar da nasarar jam’iyyar a lokacin zaben shugaban kasa na 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: ‘Yan Najeriya Za Su Yi Wa Shugabanni Hisabi a Lokacin Zaben 2023 – Osinbajo
Da yake jawabi a taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a jihar Benuwe, Ayu ya ce: “Ina kira ga kanina, Gwamna Ortom da ya dawo ya hada kai da mu domin mu yi yaki domin ceto Najeriya.
“Gwamna Ortom ba shi da inda zai je, gidansa tilo shi ne PDP kuma duk lokacin da ya zo, za mu fi jin dadin tarbarsa da dukkan gwamnonin PDP.”
Ortom ya fusata da shugabancin jam’iyyar tun bayan zaben fidda gwani na shugaban kasa na PDP a shekarar 2022.
Yana cikin kungiyar da aka fi sani da Integrity Group, mai fafutukar tabbatar da gaskiya, daidaito da adalci.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito Kungiyar Integrity Group karkashin jagorancin Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, ta yi ta kokarin ganin an sauya shugaban PDP na kasa Ayu.
Sun jaddada cewa ya kamata dan Kudu ya maye matsayin Shugaban jam’iyyar PDP na kasa domin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, ya fito ne daga Arewa.
A wani labarin kuma, NSA Ya Yiwa Shugaban INEC Alkawarin Samar Da Cikakken Tsaro a Lokacin Zabe
Yayin da ya rage kanaki 17 kacal a gudanar da babban zaben 2023, Shugaban Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, Mahmood Yakubu, ya gana da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, a ranar Talata.
Yakubu ya gana da Monguno biyo bayan ziyarar ban girma da ya kai wa gwamnan babban banki Najeriya Godwin Emefiele a baya.