Ka Zama Zakaran Gwajin Dadi, Gwamna Yahaya Bello
Gwamnan Jihar Abia Dr. Okezie Ikpeazu ya suffanta gwmana Yahaya Bello a matsayin jajircen gwmana.
KARANTA:- Gwamanan Zamfara Matawalle Ya Biya Miliyan 100 ga Dalibai Masu Rubuta WAEC
Yace hakane a ranar Juma’a yayin da yake karbar tarbar gwmana Yahaya Bello a babban birnin Jahar.
Yace tundaga shekarar 2016 har zuwa yau gwamna Yahaya Bello ya kasance Jagora wanda ya kawo cigaba ga tattalin arziqin Jahar.
Ya Kara da cewa abunda ya shafi tsaron Jahar abun a bayyane yake, yace Jahar ta zama cibiya ga sauran jahohi a halin yanzu Jahar Kogi ta zaune lafiya, yace ina maka fatan Jahar ka zata zama daya daga cikin manyan jahohi wanda tattalin arziqin su ke bunkasa.
Ya Kara da cewa ina matukar jindadin yadda kake jagoranta tare da matasa a Jahar ka ka basu dama, wanda hakan yasa kazama abun koyi agaresu kuma sunnuna zasu iya rike kowane mukami a kasa baki daya.
Gwamna Yahaya Bello shi kuma yayinda yake jawabinsa ya nuna sha’awarsa ga hadin Kai inda yake cewa duk da rikice rikicen dake faruwa a kasar Najeriya zata dawwama a matsayin kasa daya.
Gwamna suna da dangantaka sosai da Dr. Ikpeazu duk da cewa ba jam’iyyar su daya ba sannan ba yankin su daya ba ya cigaba da rike zumunci tare da sauran gwamnonin yankin.
Comments 1