Ka zauce, ba za mu ƙara jure shashancin ka ba – PDP ga Wike
Jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta sha alwashin cewa, ba za ta ci gaba da yarda da kalaman da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya le yi wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubabar.
Idan zaku tuna cewa Gwamna Wike wanda ya bukaci shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu ya yi murabus a matsayin sharadi na marawa Atiku baya a zaben da za a yi a watan Fabrairu, a lokuta da dama, ya yi Shagube ga tsohon mataimakin shugaban kasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yadda Wani Matashi Ɗan Najeriya Ya Damfari Wata Mata Maƙudan Kuɗaɗe a Indiya
A ranar Litinin, Wike, yayin da yake mayar da martani game da amincewa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi da tsohon shugaban Atiku, Olusegun Obasanjo, ya yi wa Atiku ba’a da shaguɓe, yana mai cewa dole ne wani abu ya kasance ba daidai ba.
Da yake mayar da martani, PDP a wata sanarwa da kakakin ta kuma daraktan hulda da jama’a na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, Sanata Dino Melaye, ya fitar dauke da sa hannun, ya ce Wike yaji kunya.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Ya kamata Wike ya ji kunya ganin yadda ya ke neman Atiku a kullum ta hanyar rashin mutuntawa da cin mutuncin mutumin da bai yi maka komai ba.
“Ina ba shi shawara da ya goyi bayan duk wanda yake so ya goyi bayan saboda ba za mu lamunta da son zuciya ba. Abin tambaya a nan shi ne, shin akwai wani abu da Wike bai damka wa Amaechi ba?
“Me yasa Prince Uche Secondus, Rt Hon. Austin Okpara, Sen. Lee Meaba, H:E Celestine Omehia, Chief Abiye Sikibo, Sen George Sekibo, Hon. Chinyere Igwe, da sauransu, sun bar shi ba tare da sanin ya kamata ba ga Atiku. Tabbas wani abu ba daidai ba ne a wani wuri”.
A wani labarin kuma: Zaɓen 2023 na iya jefa tattalin arzikin Najeriya cikin halin durƙushewa – Gargaɗin Masana
Idan aka waiwayi bangaren kasuwancin Najeriya a shekarar 2022, ya nuna cewa da zabe da canjin gwamnati da ke tafe a shekarar 2023, da alama bangaren zai durkushe.
Jadawalin shekarar 2022 da yadda harkar kasuwanci ta kasa ta kasance a cikin hotuna na wani lokaci da aka yi fama da hauhawar farashin kayayyaki, rashin aikin yi, talauci, rashin tsaro, rashin kyawun tsarin musayar kudaden waje, faduwar darajar Naira a kan wasu kudade, tsadar makamashi, raguwar habakar arzikin cikin gida, karancin man fetur. ambaliyar ruwa, dambarwar satar mai, yawan kudin ruwa, hauhawar basussukan jama’a, da sake fasalin tsarin Naira tare da halartar taron