Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa NLC Kwamared Ayuba Wabba ya tanka game da alwashin gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir el-Rufa’i na cewa yana neman shi ruwa a jallo.
Kwamared Wabba ya bugi kirjin cewa idan gwamnan ya isa to ya je ya kama shi yana nan jiransa.
Cikin wata gajeruwar tattaunawa da manema labarai a Shataletalen NEPA yayin da yake jagorantar dubun-dubatan yan kungiyar NLC din, Wabba ya ce wannan zanga-zanga ba wai ta kashin kai ne, a’a sai dai don al’umma.
“Ya zo ya kama ni idan ya isa, ga mu a nan muna jiran shi”
Jaridar Dimokuraɗiyya ta gani cewa dubbannin masu zanga-zangar sun killace manyan hanyoyin birnin Kaduna inda ala tilas masu ababen hawa suka sauya hanya.
Da ma dai da sanyin safiyar yau Talata ne el-Rufa’i ya bayyana buƙatar nemo Wabba ruwa a jallo, tare da sanya tukwici ga duk wanda ya gano maboyar shi.