‘Yan Kabilar Irigwe da Fulani dake rikici a Jihar Filato sun amince su rattaba hannu a yarjejeniyar zaman lafiya, bayan wani taron sulhu da suka halartar a fadar gwamnatin jihar wanda Gwamna Simon Lalong ya jagoranta.
Rahotanni daga fadar gwamnatin jihar sun ce bayan ganawar da shugabannin bangarorin suka yi daban-daban a makon jiya, Gwamna Lalong ya gana da bangarorin biyu tare inda suka tattauna batutuwa da dama da suka shafi matsalolin da ake samu a tsakanin su da kuma hanyoyin da suke ganin za a bi domin samun zaman lafiya mai dorewa.
Sanarwar da Daraktan hulda da jama’a na Gwamna Lalong, Makut Simon Macham ya rabawa manema labarai ta ce bangarorin biyu sun bayyana aniyar su ta yafewa juna akan illar da aka yi wa kowanne bangare da kuma ci gaba da zama tare a tsakanin su.
Wakilan bangarorin biyu sun kuma amince su ci gaba da ganawa a tsakanin su domin kara tattauna abin da ke haifar da matsaloli a tsakanin su kafin fitar da yarjejeniyar aiki tare.
Gwamna Lalong da ya jagoranci zaman yace gwamnati zata ci gaba da nata aikin wajen zakulo bata gari a cikin su da kuma gurfanar da su a gaban shari’a, yayin da ya shaidawa bangarorin biyu cewar bukatar zaman lafiya ya dogara ne wajen kawar da masu aikata laifuffukan dake boya a cikin jama’a.