Gwamnan Jihar Edo Mista Godwin Obaseki ya gargadi shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole, da kada ya kasa hannunsa a zaben fidda gwani da za a yi a jihar ta Edo.
Obaseki ya bayyana hakan a ranar Laraba bayan da ya kai fom din tsayawarsa takara ofishin Jam’iyyar APC na kasa dake Abuja.
https://dimokuradiyya.com.ng/zan-yi-takara-a-jamiyyar-apc-gwamna-obaseki/
“Ina jan kunnen Oshiomhole da ya cire hannunsa, ya kare mutuncinsa domin na san yana da ra’ayin a zaben da za a yi”.
Gwamnan yace ya shirya tsaf da duk irin nau’in zaben fidda gwani da za a yi, ko dai a yi kai tsaye ko kuma ba kai tsaye ba.
Bayanai na nan tafe……