Tsohon Dan Takarar Gwamnan Jihar Katsina a Karkashin Inuwar Jam’iyar APC Alhaji Garba Sani Dankani Jikan Hambali,ya bukaci Al’umar Jihar Katsina akan kada su damu da takaddamarda ke faruwa a halin yanzu ta bijiro da tsarin fito da dan takara a Kasarnan.
Jikan Hambali ya bayyana hakan ne a lokacinda yake tsokaci akan takaddamarda ke faruwa a Majalissar Kasa akan tsarin fitar da yan takara da ake so a gabatar da shi.
Mu dai fatanmu ko wane irin tsari ne za’azo da shi burinmu Allah ya bamu damar taka tamu rawar ta fuskar kawo cigaban Al’ummar Jihar Katsina , “Cewar Jikan Hambali”.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jikan Hambali ya taya ɗaukakin Al’ummar Jihar Katsina Murnar Shiga Sabuwar Shekara 2022
Abinda muke fata shine Allah SWT ya tabbatar da shigarmu fadar Gwamnatin Jihar Katsina, don haka duk tsarinda aka bijiro da shi a shirye muke muyi maraba da shi.
Jikan Hambali ya bukaci Jama’ar Jihar Katsina musamman magoya bayanshi akan kada su kadu da duk tsarinda aka zo da shi,illa iyaka su kasance masu biyayya da bin doka da oda a duk inda suka samu kansu.
Daga nan sai ya maganta akan kudurorinshi na kawo cigaban Al’umar Jihar Katsina.
Kudurorin dai sun hada da Inganta rayuwar matasa,da Noma da kiwon Lafiya da tsaro da samar da ruwan sha gami da bunkasa harkokin kasuwanci da dai sauransu.
Abinda muke da bukata shine al’uma su tayamu da addu’a Allah ya sanya mu samu damar dare madafun shugabancin jihar Katsina.
Daga karshe ya yi addu’a akan Allah SWT ya kawo karshen fitintunu dake fuskantar Jihar Katsina da Kasa baki daya domin ingantuwar Tattalin arziki.