Kada ku sake kuzo yaƙin neman zaɓe a Abia — IPOB ta gargaɗi Ƴan Takarar APC
Ƙungiyar Masu Rajin Kafa Ƙasar Biafra IPOB ta gargaɗi ƴan takarar Jam’iyyar APC na Gwamna Ikechi Emenike da Jam’iyyar sa da kada su sake suyi gangamin yaƙin neman zaɓe a Umuahia a ranar 20 ga watan Mayun Shekarar 2022.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dole mu sake gina Fatan Ƴan Najeriya — Fayemi ya gayawa APC
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa daga bakin Mai Magana da Yawun Ƙungiyar Emma Powerful.
IPOB tace Emenike bazai gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓe ba “a yayinda yayi shiru kuma ƴan bindiga suna riƙe da ƴan uwansu a Uturu”.
Sanarwar tace ” muna son mu shawarci Chief Ikechi Emenike da ƴan APC da kada su sake su gudanar da wani gangamin yaƙin neman zaɓe ba a Umuahia a gobe, Juma’a 20 ga watan Mayu na shekarar 2022, a yayinda suka yi shiru, kuma basu yi komai ba a lokacin da ƴan bindiga suka sace Ɗalibai Mata akan hanyar Okigwe/Uturu.
“Bazamu iya barin Emenike da ƴan Jam’iyyar APC su riƙa rawa da waƙoƙi a wajen taron Chidiebere, yayinda ƴan mata ke hannun ƴan bindiga.