Gabanin Babban zaben shekarar 2023, tsohon mataimakin shugaban majalisar Dattijai ta ƙasa Farfesa Ike Ekweremadu, ya buƙaci yan jarida da kada su yarda a riƙa amfani dasu domin cima ƴan siyasa mutunci akan wasu.
Ya bada shawarar a ranar Lahadi a lokacin da ya karɓi baƙuncin sabbin mambobin ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa masu aikawa da rahotanni reshen jahar Enugu, a gidan sa dake Enugu.
A lokacin da yake bayyana cewa, idan zasu tallata mutum, to suyi hakan akan al’amuran da aka tabbatar, yace kafar yaɗa labarai kada ta bari ayi amfani da’ita wajen tura labarai marassa inganci ko kuma zarge-zargen da baza suyi amfani ba.
Ekweremadu dake wakiltar Enugu ta yamma yana da damar dazai faɗi magana, amma ta zamanto wadda zata kawo cigaba ne, kamar yadda majiyar jaridar Dimokuraɗiyyar ta ruwaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar Soji SADC ta hallaka Yan bindiga 17 a Cabo Delgado na Mozambique
“A matsayina na Sanata, nayi aiki a wurare da dama, amma wurin da nake jindaɗin aiki, shine wurin bada damar magana. Na yarda da aba ƴan ƙasa damar su faɗi ra’ayoyin su, domin ba tare da hakan ba ai an mutu, kuma ba za’a sami wani cigaba ba,” inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar Soji SADC ta hallaka Yan bindiga 17 a Cabo Delgado na Mozambique
Ekweremadu ya buƙaci ƴan jarida da akoda yaushe su kasance masu amfani da dokokin aiki, a lokacin da suke gudanar da harkokin su, gami da gudanar da binciken ƙwaƙwaf a dukkanin rahotannin su.
“Na san ku shekaru da dama, amma ban taɓa tambayar wani ya rubuta wani abu na ɓatanci akan wani ba. Wannan shi ya kamata kuyi a dai-dai lokacin da muke tunkarar zaɓen shekarar 2023. Idan wani yazo ya kawo maku wani abu na zargi kuce ya bada hujjoji akan hakan.
Ekweremadu ya kuma sha alwashin bada lambar girmamawa ga dukkanin wani rahoto na ƙwaƙwaf da akayi.