Tsohuwar ma’aikaciyar BBC, Kadaria Ahmed, a ranar Litinin ta bayyana cewa yunkurin dokar da ‘yan majalisar Nijeriya ke kokarin kakabawa barazana ce ga dimokuradiyyar Nijeriya kuma barazana ce ga aikin Jarida a Nijeriya.
Kadaria Ahmed ta shaidawa majiyarmu hakan ne jim kadan da kammala wani taron gabatar da kyaututtuka na 2019 da ya gudana a garin Legas, inda ta ce wannan dokar da majlisar ke kokarin kakabawa zai take ‘yancin fadar albarkacin baki da na kafafen watsa labarai kamar yadda dokar Nijeriya ta tanadar.
Sanata Mohammed Musa na jam’iyyar APC mai wakiltar gabashin jihar Neja, shi ne ya gabatar da kudurin wannan doka gabatar majalisar, inda ya nemi da a rika yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga masu yada kalaman batanci a shafukan sada zumunta.
A cewar Sanata Musa, dokar amfani da shafukan sada zumunta za a tabbatar da shi domin tsarkake yadda ake amfani da shafukan sada zumunta a Nijeriya, amma ba wai domin a hana kafafen watsa labarai ayyukan su ba.
Kadaria Ahmed ta ce kokarin kakaba wannan dokar barazana ce ga aikin Jarida da dimokuradiyya a Nijeriya. Inda ta ce maganar yada kalaman batanci da na karya a shafukan sada zumunta, wadansu dokokin kasar sun dauke wannan.