Sanata Uba sani ya samu kyakkyawar tarba daga Al’umma a lokacin da yake kaddamar da cibiyoyin wassani na MATASA na Turunku dake a jihar Kaduna Sanatan ne ya bayyana Hakan a lokacin a Wata Sanar yana Mai cewa samu gata na musamman da karramawa a yau na kaddamar tare da mikawa ma’aikatun gwamnatin jihar Kaduna da abin ya shafa, cibiyoyin wasanni (Neighbourhood Sports Centres) a kananan hukumomin Kaduna ta Arewa, Igabi da Kaduna ta Kudu, da kuma cibiyar ICT da ke Turunku.
Sanatan yace domin saukaka wasu ayyukan da suka shafi shiyyar don samar da damammaki ga dimbin matasan jihar Kaduna har’ila yau domin baje kolin basirarsu, sanin cikakken kwarin gwiwarsu da kuma sanin ci gaban fasaha.
A wajen bikin mai kayatarwa na samu halartar kwamishinan matasa da wasanni na jihar Kaduna, da wakilan hukumar inshorar ajiya ta kasa (NDIC), jami’an jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Royal Fathers da sauran masu ruwa da tsaki.
Kammalawa da mika cibiyoyin wassani da cibiyar ICT hakika mafarki ne daya tabbata zuwa gaske. Jihar Kaduna na cike da hazaka a fannin wasanni daban-daban. Idan har aka yi amfani da fannin wasanni yadda ya kamata da kuma bunkasa shi a matsayin kasuwanci tabbas za’a zamu Wata dama da gudunmawa sosai wajen yaki da talauci da rashin aikin yi ga matasa.
Wasanni kuma wani tushe ne mai karfin gina zaman lafiya da tabbatar da wanzuwar jituwa. Ta hanyar cibiyoyin unguwanni masu hada alaka da juna matasanmu za su yi mu’amala mai kyau da fahimtar juna da kulla dangantaka mai dorewa. Cibiyar ICT za ta ba da gudummawa wajen bunkasa fasahar matasan mu a fannin fasahar sadarwa. Tattalin arzikin ilimi shine makomar duniya. Dole ne a mayar da matasanmu matsayi don su kasance masu shiga gasa a sahun duniya.
Ƙaddamar da waɗannan ayyuka wani shiri ne da gangan don haɗawa da kyakkyawan yunƙurin samar da ababen more rayuwa na Gwamna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i. Inji Sanata Uba sani.