Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ce mafi yawan al’ummar da suke kada kuri’a matasa ne da mata don haka ya ke kirga kuri’unsu don lashe zaben gwamna.
Sanata Uba Sani, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce mata da matasa suna rike da manyan mukamai a gwamnatin Gwamna Nasir El-Rufa’i.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnoni Sun Kafa Kwamitin da Zai Zauna da CBN Kan Tsarin Sauya Takardun Naira
Dan majalisar ya ci gaba da cewa, babu wata gwamnati da ta taba baiwa mata dama kuma ta ba su matsayin da ya dace a tarihin jihar Kaduna.
Dan takarar gwamnan ya bayyana haka ne a wajen taron mata da uwargidan gwamnan jihar Kaduna, Barista Asia Ahmad El-Rufa’i da Akanta Janar, Shizzer Bada suka shirya a filin wasa na Township ranar Asabar.
A cewarsa, mace ce mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, mata kuwa sune kwamishinonin shari’a, lafiya, ilimi, ayyukan jin kai da ci gaban jama’a, haka kuma kwamishinan gidaje da raya birane, ciki har da kwamishinan kananan hukumomi da Kasafin Kudi da tsare-tsare.
Sanata Uba Sani ya ci gaba da cewa mace ce shugabar ma’aikata kuma mata da dama ne shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar Kaduna.
Dan takarar gwamnan ya nuna cewa baya ga nade-naden mukamai, gwamnati mai ci ta baiwa mata tallafin kudi.
“Ma’aikatar kula da ayyukan jin kai da ci gaban jama’a ta raba Naira miliyan 600 ga mata ‘yan kasuwa da kungiyoyi, domin inganta sana’o’insu, a karkashin asusun tallafawa mata na jihar Kaduna (KADSWEF),” inji Uba Sani.
Dan takarar gwamnan ya yi alkawalin ginawa gwamnati mai ci a yanzu wajen karfafa mata idan aka zabe shi.
Sanata Uba Sani ya yi kira ga mata da su zabi jam’iyyar APC a kowane mataki na zabe mai zuwa, yana mai tunatar da cewa jam’iyyar za ta inganta rayuwar mazauna jihar Kaduna da kuma ‘yan Nijeriya baki daya.
A wani labarin kuma, Babu Gudu Babu Komawa Baya Kan Kayyade Cire Kuɗi, NFIU Ta Fadawa Gwamnoni
Hukumar kwararrun a bangaren kudi NFIU, ta ce ba za ta sauya ka’idojin kayyade kudaden da ake fitarwa a farkon wannan wata ba.
Hukumar NFIU, a ranar 5 ga watan Janairu, ta umurci bankunan kasar nan da su daina aiwatar da bukatu na kudi daga asusun jama’a, da kuma biyan kudade marasa imganci da alawus-alawus na balaguro, daga ranar 1 ga watan Maris 2023.