By Abbas Yakubu Yaura
Bayan shafevkwana 30 da tsare wani Fasto na Cocin Evangelical dake Nariya a karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, Rabaran Dauda Bature, ya halaka a hannun masu garkuwa da shi.
Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya reshen jihar Kaduna, Rev. Joseph Hayab ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.
An ce an kashe faston ne bayan da matarsa ta kai wani bangare na kudin fansa na naira miliyan 5 da masu garkuwar suka nema.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa idan za’a iya tunawa an sace Fasto Bature ne a gonarsa a ranar 8 ga watan Nuwamba, 2021,wanda masu garkuwa da mutane suka nemi da a biyasu Naira miliyan 5 a matsayin kudin fansa.
Sannan an bayyana cewa matar tasa ta je ta kai wani bangare daga cikin kudin fansa lokacin da itama suka yi garkuwa da ita.
Sai dai amma, an sake ta a ranar 6 ga watan Disamba, 2021 don ta je ta tara ƙarin kuɗi don sakin mijinta.