Wata matashiya mai suna Halima Yunusa a ranar Litinin ta maka mahaifinta a gaban wata kotun shari’a da ke zamanta a Magajin Gari a jihar Kaduna bisa zargin kin aurenta da masoyinta Mai suna Bashir Yusuf.
Halima wacce ke zaune a Kasuwan Magani a karamar hukumar Chikun ta jihar, ta shaida wa kotun cewa tana son Yusuf, amma iyayenta sun ki amincewa su auramata shi.
Mahaifin Halima, Ibrahim, wanda dan kasuwa ne, ya bayyana karara cewa yana sane da “matsananciyar soyayya” da ke tsakanin ‘yarsa da Yusuf, amma har yanzu Yusuf bai cika duk wasu wajibai na aure ba.
Mahaifin Halima ya yarda cewa Yusuf ya zo wurinsa kuma ya nuna sha’awarsa na auren ‘yarsa, amma ya ce masa ya kawo iyayensa da ‘yan uwa.
Yace Yusuf bai turo iyayen sa ba bayan kusan shekara guda.
Ya Kuma kara da cewa, bayan shekara daya Yusuf ya dawo ya dauki ‘yarsa ya gudu da ita har tsawon kwanaki uku, ya kara da cewa daga baya ya ji sun dawo.
A cewarsa, ya sanar da ‘yan sanda kuma an kama su tare da ladabtar da su.
Kana Ya ce bayan an sako su daga hannun ‘yan sanda sun gudu zuwa Abuja inda suka shafe makonni biyu.
Ibrahim ya kara da cewa daga baya ya gana da mahaifin yaron kuma sun tattauna da yawa, amma mahaifinsa ya ce ba zai bar dansa “ya auri ‘yata ba”.
“Daga karshe, mahaifinsa ya kai mu wurin hakimin kauyenmu inda aka tsara yarjejeniyoyin da mu da shaidunmu suka sanya hannu don a gargadi ’yata ta nisanci dansa,” inji shi.
Alkalin kotun, Murtala Nasir, bayan ya saurari bangarorin biyu, ya ce a shawarci mahaifin Yusuf da ya bar yaran su yi auren su.
A cewar Alkalin, “Idan ya ki, za mu yi musu aure a kotu ko da ba tare da amincewar sa ba.
Alkalin kotun, yayin da ya dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Mayu domin mahaifin Yusuf ya gurfana a gaban kotun domin yanke hukunci na karshe, ya shawarci mai karar da ta nemi gafarar iyayenta da ‘yan uwanta domin samun albarka a rayuwarta.