Mai Neman takarar gwamnan jihar Kaduna a karkashin inuwar jam’iyyar APC, Alhaji Sani Mahmud Sha’aban, ya yi barazanar ficewa daga jam’iyyar saboda rashin adalci da shugabancin jam’iyyar ke yi.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar da kodinetan yakin neman zaben shi na shiyya ta daya ta jihar.
Sani Sha’aban wanda yana daya daga cikin ‘yan takarar gwamnan Kaduna ya koka da rashin adalci da son zuciya da shugabancin jam’iyyar musamman fadar gwamnatin jihar ke yi.
“Kamar yadda nake magana da ku a yanzu, an riga an zabo wakilai daga gidan gwamnati da za su gudanar da zabe yayin zaben fidda gwani.
Ya kara da cewa, “Mafi yawan mu masu son tsayawa takara ba mu yi su ba, domin an zabe su ne a mazabu, kananan hukumomi da jiha.
Dan takarar na jam’iyyar APC ya bayyana cewa irin wannan rashin adalci zai sa jam’iyyar ta fadawuwa ne kawai a jihar.
Ya ce, “Kuma idan aka yi wani abu don sauya lamarin, toh za a bamu wani dama ne na sauya sheka daga jam’iyyar domin ba za mu iya alakanta kanmu da rashin adalci ba.
A wani labari Kuma
Muhuyi ya Jajantawa Waɗanda Fashewar Tukunyar Gas ya shafa a Kano
Ɗan Takarar Gwamnan Jahar Kano a Jam’iyyar PDP Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, ya Jajantawa Al’ummar Jahar Kano, da na Sabongari musamman waɗanda Fashewar Tukunyar Gas ya shafa a Kano.
Wannan na Ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai Taimaka mashi akan Kafafen Yaɗa Labaru dasu zama masu haƙuri a lokacin da suke fita zuwa gudanar da harkokin su na yau da Kullum.
Barista Magaji yayi nuni dacewa irin muhimmiyar rawar da Kano ke takawa wajen cigaban harkokin Najeriya bazai iya misaltuwa ba, sakamakon ƙabilu da dama a Jahar.
Yayi kira ga Kowa da ya cigaba da Addu’o’i domin samun zaman lafiya da lumana a Jahar, a yayinda aka tunkari Babban Zaɓen.
Jigo a Jam’iyyar PDP yace Fashewar Tukunyar Gas babban abune da ya cancanci zubar da hawaye, saboda Al’umma su cigaba da haɗa kansu, a yayinda aka haɗa hannu domin ciyar da Jahar Kano a matakin gaba.
Magaji ya kuma yi kira ga kowa da kowa daya guji yaɗa labarun ƙarya akan lamarin koda Fashewar Tukunyar Gas ne ko kuma Fashewar Bom.
Ya kuma yi ta’aziyya ga waɗanda suka rasa ƴan uwansu sakamakon wannan mummunan lamari, tare da yin addu’a ga Allah daya sanya wannan shine na ƙarshe da zai faru anan gaba.